Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya kuduri aniyar tabbatar da cewa zaɓen 2027 zai kasance mafi gaskiya da sahihanci fiye da na 2023. Ya bayyana haka ne a Abuja yayin taro da tawagar Tarayyar Turai (EU), inda ya ce Majalisar Dokoki ta ƙasa na aiki kan gyaran Dokar Zaɓe ta 2022 domin inganta tsarin zaɓe.

Abbas ya ce majalisar ta tattara matsalolin da aka gano a zaɓen 2023, musamman na masu sa ido, domin yin sauye-sauyen doka da tsarin mulki. Ya ce za a ware batun zaɓe a matsayin muhimmin abu guda da za a kammala kafin Disamba, ciki har da samar da kujeru ga mata da masu nakasa, ba wa sarakunan gargajiya rawar doka, da gudanar da zaɓuka a rana guda.

Shugaban tawagar EU, Barry Andrews, ya yaba wa ƙoƙarin majalisar. A zaɓen 2023 an fuskanci matsaloli kamar jinkirin isar kayan zaɓe da matsalolin BVAS, wanda ya sa gwamnati ke shirin tabbatar da cewa zaɓen 2027 zai kasance mafi inganci da sahihanci.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version