Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da shirin biyan bashin wutar lantarki na Naira tiriliyan 3.3 domin warware matsalolin da suka addabi sashen lantarki tsawon sama da shekaru goma. Sanarwar ta fito ne daga mai ba shi shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, wanda ya ce an kammala tantance bashin da aka tara daga 2015 zuwa 2025.

A cewar gwamnati, tuni an fara aiwatar da shirin, inda kamfanonin samar da wuta 15 suka rattaba hannu kan yarjejeniyar karɓar kusan Naira tiriliyan 2.3, yayin da aka tara Naira biliyan 501 don fara biyan kuɗin. Daga ciki, an riga an biya Naira biliyan 223, kuma ana sa ran hakan zai inganta samar da wutar lantarki a ƙasa.

Gwamnatin ta bayyana cewa wannan mataki zai ƙara ƙarfin samar da wuta, jawo zuba jari da samar da ayyukan yi, tare da inganta ayyukan kasuwanci. Sai dai rahotanni sun nuna cewa jimillar bashin da ake bin sashen na iya kaiwa sama da Naira tiriliyan 6.8, lamarin da ke nuna bambanci da adadin da gwamnatin ta amince da shi.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version