Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga gwamnonin jihohin ƙasar nan da su gaggauta aiwatar da hukuncin kotun ƙoli da ya bai wa ƙananan hukumomi ƴancin karɓa da tafiyar da kuɗaɗensu kai tsaye.
Tinubu ya yi gargaɗin cewa duk gwamnan da ya ƙi bin wannan umarni zai tilasta masa amfani da wata doka ta musamman da za ta ba shi ikon aikawa ƙananan hukumomi kuɗaɗensu kai tsaye daga asusun rabon arzikin tarayya. Ya bayyana hakan ne a taron majalisar zartarwar jam’iyyar APC karo na 15 da aka gudanar a Abuja.
Kotun ƙoli, a ranar 11 ga watan Yulin 2024, ta yanke hukuncin da ya haramta riƙe kuɗaɗen ƙananan hukumomi da gwamnatocin jihohi ke yi, inda alƙalan kotun bakwai suka amince cewa hakan ya saɓawa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya.
