Majalisar Dattawa ta samu sabuwar buƙata daga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin amincewa da ɗaukar rancen N1.15 tiriliyan daga cikin gida, domin rufe gibi a kasafin kuɗin shekarar 2025. Wannan buƙatar ta zo ne a cikin wata wasiƙa da shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta yayin zaman majalisar. An tura buƙatar zuwa kwamitin da ke kula da basussuka na cikin gida da na waje domin nazari, tare da umarnin su dawo da rahoto cikin mako ɗaya.

Wannan sabon rancen ya biyo bayan amincewar majalisar kwanaki kaɗan da suka gabata ga wani sabon rance na dala biliyan $2.847bn, ciki har da $500m na Sukuk, wanda za a yi amfani da su wajen saka hannun jari a kan muhimman ayyukan gwamnati da kuma biyan bashin Eurobond da ya kusa ƙarewa. A cewar kwamitin basussuka, wannan tsarin rancen yana ƙarƙashin tsare-tsaren kasafin 2025 da aka riga aka tsara domin tabbatar da ci gaba da ayyukan gwamnati ba tare da tsaiko ba.

Sai dai wannan sabon yunkurin ya sake tayar da muhawara a tsakanin masana da jama’a, ganin yadda bashin Najeriya ya riga ya haura N97 tiriliyan a tsakiyar shekarar 2025, a cewar Hukumar Kula da Basussuka ta Kasa (DMO). Wasu sun nuna damuwa cewa cigaba da ci bashin na iya jefa tattalin arzikin ƙasar cikin haɗari, yayin da gwamnati da wasu ‘yan majalisa ke cewa rancen yana da muhimmanci wajen ginawa da farfaɗo da tattalin arziki.

Shugabannin kwamitoci daban-daban a majalisar sun kare wannan rance, suna mai cewa ya dace da tsarin kasafin 2025 kuma zai taimaka wajen gujewa ɗaukewar ayyuka ko gaza biyan bashin ƙasashen waje. Wasu kuma sun yi nuni da cewa idan aka yi amfani da rance cikin tsari mai kyau, zai iya rage matsalolin rashin aikin yi da kuma inganta manyan ayyukan raya ƙasa.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version