Dr. Kabiru Turaki (SAN) daga jihar Kebbi ya zama sabon shugaban jam’iyyar PDP bayan ya samu kuri’u 1,516 a babban taron zaben jam’iyyar da aka gudanar a Ibadan, inda ya doke Garuba Lado mai kuri’u 41. A cewar kwamitin shirya taron karkashin Sanata Ben Obi, jimillar wakilai 2,745 ne aka tantance, yayin da kuri’u 275 suka lalace. Haka kuma wasu kujeru 17 an yi takara kansu ba tare da hamayya ba, ciki har da na Mataimakin Sakataren Tsare-Tsaren Jam’iyya da Solarin Adekunle ya lashe.

A jawabinsa na karɓar shugabanci, Turaki ya sha alwashin kawo ƙarshen abin da ya kira zalunci da murdawa cikin jam’iyyar, yana mai cewa sabon shugabanci zai yi aiki da muradun mambobi ne ba tare da tauye wa kowa dama ba. Ya jaddada cewa za su bude kofa su saurari ‘yan jam’iyya, tare da tabbatar da adalci, gaskiya da daidaito domin farfaɗo da martabar PDP a fagen siyasa.

Turaki ya ce PDP na cikin mawuyacin hali, amma sabon shugabanci ya kuduri aniyar magance matsalolin da ke ci mata tuwo a kwarya. Ya ce za su fara tuntubar jiga-jigan jam’iyyar da ke da ƙorafe-ƙorafe ko waɗanda suka fice, domin su dawo su taimaka wajen “ceton dimokuraɗiyyar Najeriya daga rugujewa.”

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version