Jam’iyyar ADC ta soki Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan kalamansa na cewa a shirye yake ya yi “faɗan ƙarshe” a fagen siyasa, tana mai cewa ya kamata ya fi mayar da hankali wajen yaƙi da rashin tsaro.
A wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran jam’iyyar na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya sanya wa hannu, ADC ta ce bai dace Tinubu ya yi irin waɗannan kalamai ba yayin da wasu sassan ƙasar ke fama da ta’addanci, ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane.
Jam’iyyar ta yi nuni da harin da aka kai ƙauyen Naridon da ke Kaduna, inda ta ce aƙalla mutum 30 suka rasa rayukansu, tana mai cewa ya kamata shugaban ya fi mayar da hankali wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, maimakon mayar da martani ga ’yan adawa.
ADC ta ce ’yan Najeriya sun zaɓi Tinubu ne domin ya yaƙi ’yan ta’adda, ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane, ba jam’iyyun adawa ba. Ta ƙara da cewa ana samun nasara a zaɓe ne ta hanyar kyakkyawan aiki, tana mai jaddada cewa manyan maƙiyan Najeriya su ne ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane.
