Aƙalla mutum 13 ne suka rasa rayukansu bayan wasu ’yan bindiga sun kai hari wani ƙauyen manoma da ke jihar Benue, a yankin tsakiyar Najeriya.
Harin ya zo ne makonni bayan wasu hare-hare a kudancin jihar da suka kashe aƙalla mutum 18, lamarin da ya jawo zanga-zangar mazauna yankin kan abin da suka bayyana a matsayin ƙara tabarbarewar tsaro.
Shaidu sun ce sama da mutum 30 ɗauke da makamai, a kan babura, sun shiga ƙauyen Efeyi da ke Ugboju, Ƙaramar Hukumar Otukpo, ranar Talata. Sun yi harbe-harbe tare da amfani da adduna wajen sare mutane, lamarin da ya tilasta wa mazauna tserewa.
Mazauna yankin sun zargi maharan da kasancewa makiyaya, amma babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da hakan. Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC cewa ya ƙirga gawarwaki 13 da aka kai ɗakin adana gawa na asibiti.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version