Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta kasa gurfanar da wanda ya kira kansa Darakta-Janar na Hukumar Presidential Foreign Investment Promotion Council (PFIPC), Adeyemi Adeniyi, a gaban Kwamitin Majalisar Wakilai da ke binciken ayyukan hukumar da ake zargin ba ta da tushe.

Maimakon haka, wakilan ’yan sandan sun shaida wa kwamitin cewa suna buƙatar umarnin kotu a rubuce da zai ba su damar fitar da Adeyemi daga hannunsu domin gurfanar da shi a gaban ’yan majalisar.

Kwamitin da ɗan majalisa Yusuf Gagdi daga APC mai wakiltar Filato ke jagoranta, ya umarci Babban Sufeton ’Yan Sanda, Olatunji Disu, a ranar Litinin da ya gurfanar da Adeyemi a gaban kwamitin kafin tsakar ranar Laraba.

Sai dai ’yan sandan sun ce Adeyemi na hannunsu ne bisa sahihin umarnin kotu na ci gaba da tsare shi, don haka ba za su iya gurfanar da shi ba tare da samun izinin kotu ba. Sun kuma buƙaci kwamitin ya samar da umarnin kotu ko wata takardar izinin doka da za ta ba su damar yin hakan ba tare da karya umarnin kotun ba.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version