Hukumar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta fara bincike kan mummunan lamarin da ya faru a unguwar Tudun Yola, ƙaramar hukumar Gwale, inda aka kashe mata biyu tare da ƙona gidansu. Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna, ya tabbatar da faruwar al’amarin, yana mai cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin kisan.
Mazauna unguwar sun ce matar farko an same ta da alamar an soke ta kafin wutar ta kama cikin gidan, yayin da aka tarar da matar ta biyu a cikin bandaki a rufe, kuma ta riga ta mutu lokacin da aka fasa ƙofar. Dukkan matan biyu mata ne ga Alhaji Ashiru Shu’aibu Usaini, kuma abin ya faru ne da rana tsaka yayin da mijin da yaransu ba su gida.
Ɗan gidan, Anas Shu’aibu, ya ce sun tarar da gawar ɗaya daga cikin matan ta ƙone, sannan suka gano ta biyun a bandaki bayan ta mutu. Ya ce lamarin ya gigita su kuma suna roƙon hukuma ta tabbatar an cafke duk wanda ke da hannu a wannan aika-aikan.
Wannan kisa ya biyo bayan jerin wasu mummunan al’amura da aka rika samu a Kano cikin ‘yan watannin baya, ciki har da kama wanda ake zargi a kisan Rumaisa Haruna da aka yi a Farawa a watan Afrilu. Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da cewa za ta tura ƙarin jami’ai da kuma tabbatar da bin diddigin duk wani bayani da zai kai ga kama masu hannu.
