Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa yana iya janye burinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027 idan har hakan ya zama dole, domin ya mara wa matashi baya.
Atiku, wanda yanzu ya zama jigo a jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), ya bayyana haka ne a cikin wata hira da ya yi da BBC Hausa a ranar Laraba 01 ga Oktoba.
Da aka tambaye shi ko zai tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027, Atiku ya ce har yanzu lokaci bai yi ba, yana mai jaddada cewa abin da ya fi mai da hankali kai a yanzu shi ne ƙarfafa haɗin kan jam’iyyar ADC.
“Lokaci bai yi ba. Idan lokaci ya yi, zan yanke shawara. Abin da muke yi yanzu shi ne ya ƙasa za ta cigaba,” in ji shi.
Ya kara da cewa idan wani ɗan takara matashi ya bayyana ya kuma kayar da shi a zaben fidda gwani, zai amince da hakan tare da mara masa baya da kuma jagorantar sa.
“Idan ɗan takara matashi ya doke ni, zan yarda in kuma goyi bayansa da cikakken ƙwarin gwiwa, sannan in yi masa jagora. ” in ji Atiku.
Ya bayyana cewa ADC na bai wa matasa da mata muhimmanci, yana mai cewa wannan shi ne babban ginshiƙin jam’iyyar.
“Jam’iyyarmu tana bai wa matasa da mata gurbi na musamman. Wannan shi ne babban abin da muke maida hankali a kai,” Atiku ya ƙara da cewa, ya kamata matasa su shiga harkokin siyasa sosai tare da neman mukamai lokacin zaɓe.
