Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen cewa za a fuskanci yanayi mai ɗauke da hazo da ruwan sama a wasu sassan ƙasar daga Litinin 27 zuwa Laraba 29 ga Oktoba. Hukumar ta bayyana hakan ne cikin wani rahoto da ta fitar a ranar Lahadi, inda ta shawarci al’umma da su kasance cikin shiri don kauce wa matsalolin da irin waɗannan yanayi kan haifar.

NiMet ta ce ana sa ran samun hazo mai ɗaukar kwanaki uku a jihohin Borno, Yobe, Zamfara, Jigawa, Kano, Katsina, da wasu yankunan arewacin Kaduna. Wannan, a cewar hukumar, na iya shafar zirga-zirgar jiragen sama da motoci, musamman a safiya.

A lokaci guda, hukumar ta yi hasashen samun ruwan sama mai ɗauke da tsawa a wasu yankunan jihohin Taraba da Adamawa, yayin da ake sa ran yanayin rana mai ɗumi a wasu sassan arewa ta tsakiya.

Haka kuma, NiMet ta bayyana yiwuwar ruwan sama a wasu yankunan Nasarawa, Kogi, da Babban Birnin Tarayya Abuja, tana mai jan hankalin manoma da masu zirga-zirga su ɗauki matakan kariya daga illolin sauyin yanayi.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version