Rundunar Ƴan Sandan Najeriya ta sanar da cewa za ta ci gaba da tilasta bin dokar mallakar lasisin amfani da gilashin mota mai duhu daga ranar 2 ga Janairu, 2026, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a ƙasar. Sanarwar ta fito ne daga jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Benjamin Hundeyin, a ranar 15 ga Disamba, 2025, inda ya ce duk wanda bai mallaki sahihin lasisi ba zai fuskanci kame da hukunci.

Sai dai ƙungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) ta soki matakin, tana mai cewa ya saɓa wa hukuncin kotu da ya dakatar da aiwatar da dokar har sai an kammala shari’ar da ke ƙalubalantar halaccinta. NBA ta bayyana cewa ci gaba da aiwatar da dokar kafin hukuncin ƙarshe na kotu na nuna raina doka, tare da gargadin cewa hakan na iya ƙara nauyi ga talakawa da kuma buɗe ƙofa ga cin hanci da rashawa.

Tun a watan Afrilu 2025 ne rundunar ƴan Sanda ta ƙaddamar da dokar, wacce ta bukaci ‘yan Najeriya su yi rijista ta intanet domin samun lasisin amfani da gilashin mota mai duhu. An fara tsara fara aiwatar da dokar a ranar 1 ga Yuni 2025, amma daga bisani aka ɗage zuwa 2 ga Oktoba saboda korafe-korafen jama’a. NBA ta sake nanata buƙatarta ga ƴansanda da su dakatar da duk wani mataki na aiwatar da dokar har sai kotu ta yanke hukunci na ƙarshe.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version