Tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari, ta bayyana cewa rashin lafiyar da ta tilasta wa marigayi mijinta, Muhammadu Buhari, yin dogon hutun jinya a shekarar 2017 ba ta da alaƙa da guba ko wata cuta ta asiri, kamar yadda ake ta yaɗa jita-jita a wancan lokaci. Ta ce tushen matsalar shi ne lalacewar tsarin ciyarwa da kula da lafiyarsa bayan shigarsu Aso Rock, sakamakon tsoma bakin wasu da kuma jita-jitar cikin fadar.

Aisha Buhari ta bayyana cewa tun da fari tana kula da abincin Buhari bisa tsari na musamman, inda ake ba shi abinci da ƙarin sinadarai (supplements) a lokuta dabam-dabam na rana, abin da ke taimaka masa samun ƙarfi duk da shekarunsa. Sai dai ta ce bayan shigarsu Villa, jita-jitar cewa tana shirin cutar da shi ta sa an daina bin tsarin, har ta kai ga “wani lokaci ana tsallake abinci, ana dakatar da ƙarin sinadarai,” lamarin da ya raunana jikinsa ƙwarai.

Wannan bayani ya fito ne a cikin sabon littafin tarihin Buhari mai suna “From Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari,” wanda Dr. Charles Omole ya wallafa, aka kuma ƙaddamar da shi a Fadar Shugaban Ƙasa. Kakaki24 ta ruwaito cewa Aisha Buhari ta jaddada cewa rashin tsari da kulawa ne ya jawo matsalar, ba wani shiri na guba ko asiri ba, tare da ƙaryata jita-jitar da ta daɗe tana yawo game da lafiyar tsohon shugaban ƙasar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version