Tsohon Babban Alkalin Ƙasa, Mai Shari’a Ibrahim Tanko Muhammad (mai ritaya), ya rasu yana da shekaru 71, a ranar Talata, 16 ga Disamba, 2025, bayan fama da doguwar jinya a kasar Saudiyya.

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed, ya tabbatar da rasuwar ta hannun mai ba shi shawara kan yaɗa labarai, inda ya bayyana marigayin a matsayin ginshikin shari’a wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare doka da adalci a Najeriya. Ya ce Tanko Muhammad ya yi aiki a manyan kotuna har zuwa zama Babban Alkalin Ƙasa daga 2019 zuwa 2022.

Gwamnan ya ƙara da cewa an karrama marigayin da lambar yabo ta GCON saboda gudunmawar da ya bayar a fannin shari’a. Ya miƙa sakon ta’aziyya ga iyalansa da al’ummar Najeriya baki ɗaya, tare da addu’ar Allah Ya gafarta masa, Ya kuma ba iyalansa haƙuri da juriyar rashinsa.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version