Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta tabbatar da kisan wani mutum mai suna Ladan Malam Zubairu a Asubahin Litinin 15 ga Disamba, 2025. a Masallacin Yusuf Garko dake Maraba Quarters, Hotoro. Shaidun gani da ido sun bayyana cewa wasu mazauna unguwar sun bi wanda ake zargi, inda kuma tuni shi ma suka kashe shi, tare da kona gidansa.
Tuni Rundunar Ƴansanda ta tura jami’an tsaro don tabbatar da zaman lafiya a unguwar. A yayin bincike, an gano makogaron ladanin a aljihun wanda ake zargin, kuma tuni aka kai gawarwakin biyu zuwa Asibitin Koyarwa na Mohammed Abdullahi Wase Kano don gudanar da autopsy.
Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce za a gudanar da cikakken bincike don kamo duk wanda ke da hannu a wannan mummunan lamari, tare da rokon jama’a da su ba da hadin kai da bayar da duk wani bayani da zai taimaka, wanda za a kiyaye sirrinsa.
