Shugaban jam’iyyar APC a jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas Sanusi, ya ce jam’iyyarsu a shirye take wajen karɓar Gwamna Abba Kabir Yusuf bayan ficewarsa daga NNPP, inda ya bayyana siyasa a matsayin wasan ƙididdiga, kuma duk wanda ya shigo jam’iyya ƙari ne ga ƙarfinta a zaɓe.
Da yake magana kan batun tikitin kai tsaye, Abbas Sanusi ya ce ba matsala ba ce a yanzu, domin har yanzu ana jiran kammala dukkan matakan shigowar gwamnan da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa da ke tare da shi. Ya ce bayan an kammala komai, APC za ta zauna ta tsara hanya da za ta amfanar da kowa ba tare da haifar da rikici tsakanin tsofaffi da sababbin mambobi ba, domin burin jam’iyyar shi ne cin nasara a zaɓen 2027.
Dangane da jinkirin sauya sheƙar gwamnan, shugaban APC na Kano ya ce dukkan rahotannin da suka rika yawo a baya jita-jita ne kawai, domin sauya sheƙa ba abu ba ne da ake yi cikin gaggawa. Ya ƙara da cewa hakan na buƙatar shawarwari masu zurfi, sannan ya shawarci mambobin APC da masu shigowa jam’iyyar da su fifita zaman lafiya da haɗin kai domin ci gaban jam’iyya da ƙasar baki ɗaya.
