Fitaccen malamin addinin Musulunci da ke Jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce zai iya goyon bayan ƙungiyoyin Boko Haram da (IPOB), idan har suna shirye ajiye makamai, kuma sun yarda zasu tattauna da gwamnatin Najeriya.
Gumi ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi, inda ya ce, tattaunawa ita ce hanya mafi dacewa wajen samar da zaman lafiya. Ya ƙara da cewa, idan waɗannan ƙungiyoyi sun amince su zauna teburin sulhu domin tattaunawa da da gwamnati, shi a shirye yake ya mara musu baya domin samun mafita ba tare da tashin hankali ba.
Malamin ya kuma yi zargin cewa gwamnatin Najeriya ta san sunaye da wuraren da ‘yan ta’adda ke buya. Ya ce matsalar tsaro ba za a magance ta da ƙarfin soja kaɗai ba, yana mai jaddada buƙatar inganta ababen more rayuwa kamar hanyoyi, wutar lantarki, kiwon lafiya da ilimi domin rage matsalolin tsaro a ƙasar.


