Organisation of Islamic Cooperation ta yi Allah-wadai da harin da ‘yanbindiga suka kai a jihar Zamfara a ranar 21 ga Fabrairu, 2026, wanda ya yi sanadin kashe fararen hula tare da sace mata da yara. Ƙungiyar ta bayyana harin a matsayin mai muni da ya saɓa wa dukkan ka’idojin ɗan adam.
A cikin sanarwar da ta fitar, ƙungiyar ta nuna cikakken goyon baya ga gwamnatin Najeriya da al’ummarta, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda abin ya shafa. Ta kuma yi addu’ar samun sauƙi ga waɗanda suka ji raunuka sakamakon harin.
Ƙungiyar ta buƙaci a sako matan da yaran da aka sace ba tare da wani sharaɗi ba domin su koma gidajensu lafiya. Haka kuma ta jaddada cewa ba za ta taɓa amincewa da ayyukan ‘yanbindiga ba, tana mai cewa za ta ci gaba da tallafawa ƙasashen membobinta wajen yaƙi da irin waɗannan hare-hare.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version