Kwamitin Kula da Kasafin Kudin Majalisar Wakilai ta Amurka ya shirya babban taron haɗin gwiwa a ranar Talata, ƙarfe 10:00 na safe agogon Washington, domin tattauna zargin cin zarafin Kiristoci a Najeriya. Sanarwar ta fito ne daga dan majalisa Riley Moore ta shafinsa na X, inda ya tabbatar da cewa za a gudanar da taron cikin gaggawa.

Taron zai gudana ne a karkashin jagorancin Mario Díaz-Balart, Mataimakin Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi kuma Shugaban Kwamitin Kula da Tsaron Kasa. Za a samu halartar mambobin kwamitocin Kasafi, Harkokin Waje da kuma Sabis na Kudi domin nazari mai zurfi. Manufar ita ce tattara bayanai kan hare-hare da kisan Kiristoci a sassan Najeriya.

Bechi Hausa ta gano cewa bayanin da za a samu zai zama ginshiƙi wajen rubuta rahoto na musamman da zai taimaka wa majalisar Amurka yanke mataki. Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara tattaunawa kan tsaro tsakanin Amurka da Najeriya, musamman ganin karuwar harin ’yan bindiga a arewacin ƙasar.

Rahoton da za a fitar na iya taka rawa wajen karfafa sabon tsarin haɗin gwiwa tsakanin kasashen biyu. Masana na ganin taron zai kara matsa lamba kan hukumomin Najeriya su kawo karshen cin zarafi a yankunan da ake fama da rikice-rikice. Ana ci gaba da jira a ga irin shawarwarin da majalisar Amurka za ta dauka bayan taron.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version