Rundunar ’yan sandan jihar Adamawa ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da aikata laifin garkuwa da mutane da barazana a unguwar Sarau Belel da ke ƙaramar hukumar Maiha ta jihar.

 

Kakakin rundunar, SP Suleiman Nguroje, ya bayyana cewa kamen ya biyo bayan ƙorafin da wani mazaunin ƙauyen Sagal, Emmanuel Daniel, ya shigar a ranar 26 ga Disamba 2025, inda ya ce ana yi masa barazanar sace shi. Ya kuma zargi mutanen da cewa su ne suka sace ƙaninsa Joshua Daniel da ya ɓace tun Nuwamba 2024.

 

Nguroje ya ce Kwamishinan ’yan sanda, Dankombo Morris, ya umarci jami’an yankin Sarau Belel da su kai samame cikin gaggawa, lamarin da ya kai ga cafke waɗanda ake zargin. Ya ƙara da cewa mutanen sun amsa laifin, kuma an mika shari’ar ga sashen yaƙi da garkuwa da mutane domin zurfafa bincike da gurfanar da su bisa doka.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version