Gwamnatin Tarayya ta tabbatar cewa za ta fara aiwatar da sabbin dokokin haraji daga ranar 1 ga watan Janairu, 2026, domin sauƙaƙa wa ’yan Najeriya da bunƙasa tattalin arziki. Shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Manufofin Kuɗi da Gyaran Haraji, Taiwo Oyedele, ya bayyana haka bayan gabatar da rahoto ga Shugaba Bola Tinubu a Legas.

Oyedele ya ce an riga an fara aiwatar da dokoki biyu daga cikin huɗu, yayin da sauran biyun za su fara aiki a watan Janairu. Ya ƙara da cewa gwamnati ta shafe watanni tana shirin aiwatar da dokokin ta hanyar horo, tsare-tsare da wayar da kan jama’a, inda manufar gyaran ba wai tara kuɗi ba ne, amma don tabbatar da adalci da ƙarfafa tattalin arziki.

Gwamnatin ta nuna shirin yin aiki tare da Majalisar Dokoki wajen magance duk wata matsala da ta taso kan sabbin dokokin, tare da tabbatar da cewa bin doka zai amfanar da kowa, musamman ma talakawa da kanana da matsakaitan ’yan kasuwa.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version