Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Yahaya, ya nuna alhininsa a kan hadarin mota da ya kashe mutane bakwai daga ƙauyen Lawanti a Karamar Hukumar Akko, yayin da suke kan hanyarsu zuwa Maiduguri, Jihar Borno domin halartar bikin aure.
A cikin sanarwa da Daraktan Harkokin Yada Labarai na Gwamnatin Gombe, Ismaila Misilli, ya sanya hannu, Gwamna Yahaya ya bayyana wannan lamarin a matsayin babban rashi da ya shafi iyalai da al’ummar Lawanti baki ɗaya. Ya ce babu kalmomi da za su iya ta’azantar da waɗanda suka rasa ‘yan uwansu cikin wannan baƙin ciki.
Gwamnan ya yi ta’aziyya ga iyalan mamatan, musamman Sarkin Jalingo, Bello Hassan Babangida, wanda ya rasa ‘yar’uwarsa da ɗiyarta; Idris Lawanti Maigari, wanda ya rasa ‘yarsa; da kuma Idris A. Isah Lawanti, mai wakiltar Akko Ward, wanda shima ya rasa dangi. Yahaya ya roƙi Allah Ya ba su juriya da haƙuri, Ya gafarta wa mamatan, kuma Ya sanya su Aljannatul Firdaus.
