Wasu da ake zargin ‘yan ta’addan Boko Haram da abokan aikinsu sun kona motoci uku dauke da kifi a yankin Mile-40 na karamar hukumar Magumeri a jihar Borno, yayin wani hari da suka kai da misalin karfe 1:00 na rana a ranar Alhamis, 20 ga Fabrairu, 2026. Rahotanni sun ce direbobin suna kan hanyarsu ta kai kifin zuwa birnin Maiduguri kafin maharan su tare su tare da kona motocin gaba daya.

Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa dukkan direbobin sun tsira da rayukansu, amma motocin guda uku — biyu kirar Peugeot J5 da kuma wata motar bas — sun kone kurmus. Wani direba ya bayyana cewa sun gudu cikin daji domin tsira, amma ya kalli yadda aka kona motarsa wadda ita ce hanyar samun abincinsa, yana mai kira ga gwamnati ta dauki mataki domin kare su.

Rahoton da Daily Trust ya wallafa, ya nuna cewa hare-haren kan motocin dakon kaya sun karu a baya-bayan nan, inda ‘yan ta’addan ke tare motoci, su wawashe kaya tare da kona su. Direbobin sun ce rashin isassun jami’an tsaro a hanyar ne ya kara bai wa maharan damar aikata wadannan hare-hare ba tare da tangarda ba.

Direbobin sun kuma yi gargadin cewa idan gwamnati ba ta dauki matakin gaggawa ba, harkokin kasuwancin dabbobi da kayan abinci a yankin za su durkushe. Sun bukaci a kara tura sojoji a kan hanyar domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a, suna mai cewa da dama daga cikin masu motoci sun daina amfani da hanyar saboda fargabar hare-haren ‘yan ta’adda.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version