Wani jami’in ɗan sanda mai mukamin kurtu a Jihar Borno, Muhammad Alhaji Muhammad, ya mayar da Naira miliyan 2.6 da aka yi kuskuren tura masa asusun banki.
Ya ce ya ɗauki matakin ne domin kare martabar Rundunar ’Yan Sanda ta Najeriya.
Rahotanni sun ce ya samu kuɗin ne ba zato ba tsammani ta hanyar manhajar Moniepoint, amma nan da nan ya mayar da su ga mai su.
Matakin nasa ya jawo yabo daga jama’a, inda wasu suka bayyana shi a matsayin jami’i mai gaskiya da amana.
Kakakin rundunar a Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa Kwamishinan ’yan sanda ya gayyaci jami’in domin yaba masa.
An bayyana abin a matsayin kyakkyawan misali na gaskiya da zai ƙara ƙarfafa amincewar jama’a ga jami’an tsaro.


