Al’ummar Farin-Ruwa da ke ƙaramar hukumar Shanono a Jihar Kano sun roƙi gwamnatin tarayya da ta jihar su kawo musu ɗaukin gaggawa domin dakile hare-haren ‘yan bindiga da ke ƙara kamari a yankin. Shugaban al’ummar garin kuma shugaban kwamitin tsaro, Alhaji Yahaya Bagobiri, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Kano ranar Alhamis 23 ga Oktoba.

Bagobiri ya bayyana cewa hare-haren sun yi sanadiyyar rasuwar mutane da dama tare da sace dabbobi fiye da 1,600 da dukiyoyin jama’a. Ya ce ƙauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Farin-Ruwa, Kuraku, Gorantuse, Saure, da Shadu, inda mazauna wuraren ke tserewa zuwa Kano da sauran wurare domin tsira da rayukansu.

A cewarsa, ‘yan bindigar na shigowa ƙauyukan a kowane lokaci — safiya, yamma ko dare — inda suke kai farmaki cikin sauƙi ba tare da wata tsangwama ba. Ya kuma bayyana cewa a wani hari na baya-bayan nan, an sace shanu sama da 40 tare da jikkata mutane da dama, yayin da wani da aka yi garkuwa da shi ya biya naira miliyan 15 kafin a sake shi.

Shugaban al’ummar ya koka da ƙarancin jami’an tsaro a yankin, inda ya bayyana cewa a wani harin da aka kai kwanakin baya, ‘yan bindigar sun shigo da babura kusan 50. Ya roƙi Gwamna Abba Kabir Yusuf da Shugaba Bola Tinubu su ɗauki mataki, tare da kira ga ‘yan majalisar da ke wakiltar Bagwai/Shanono su ƙara jajircewa wajen kawo karshen matsalar tsaro a yankin.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version