Wata kotun majistare da ke Kuje, Abuja, ta bayar da belin mai wallafa jarida kuma ɗan gwagwarmaya, Omoyele Sowore, da lauyan jagoran ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, wato Aloy Ejimakor, da kuma ɗan’uwan Kanu, Prince Emmanuel Kanu, tare da wasu mutum 10. An bayar da belin ne a kan kuɗin ₦500,000 kowannensu, tare da masu tsaya musu guda biyu.

Rahoton PUNCH Online ya bayyana cewa, an gurfanar da mutum 13 ɗin ne bisa zargin tada hargitsi da tayar da hankalin jama’a, bayan zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow da aka gudanar a Abuja ranar Litinin, 20 ga Oktoba.

A cewar rahoton, Ejimakor, Emmanuel Kanu, da sauran masu zanga-zangar an cafke su a lokacin taron sannan aka tsare su a gidan gyaran hali na Kuje, yayin da Sowore kuma aka kama shi ne a ranar 23 ga Oktoba a harabar babbar kotun tarayya da ke Abuja, bayan ya halarci zaman shari’ar Kanu domin nuna goyon baya.

Kotun ta amince da buƙatar belin da lauyoyin suka nema, inda ta umurci duk masu laifin su cika sharuddan belin kafin su samu ‘yanci, yayin da shari’ar ta ci gaba da jiran cikakken sauraro a wani lokaci na gaba.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version