Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sanar da cewa za ta raba naira biliyan 32.9 ga jihohi da cibiyoyin lafiya kafin ƙarshen watan Oktoba, domin inganta harkokin kiwon lafiyar jama’a a fadin ƙasar. Wannan mataki na cikin shirin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na inganta walwalar al’umma da tabbatar da cewa ‘yan Najeriya na samun ingantattun ayyukan lafiya a matakin farko.

Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, Farfesa Muhammad Pate, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka fitar ranar Laraba, yayin ƙaddamar da sabon tsarin Asusun Lafiya na Matakin Farko, wato Basic Health Care Provision Fund (BHCPF 2.0). Sabon tsarin ya mayar da hankali kan gaskiya, inganci da kuma biyan sakamako bisa la’akari da aikin da aka gudanar.

Farfesa Pate ya ce wannan tsari ya biyo bayan umarnin Shugaba Tinubu ne na tabbatar da gaskiya da ingantaccen amfani da kuɗaɗen gwamnati da na abokan hulɗa. Ya kara da cewa sabon tsarin zai tabbatar da cewa kuɗin da aka ware za a yi amfani da su yadda ya dace wajen samar da kayan aiki da inganta ayyukan lafiya a asibitocin matakin farko.

A cewar gwamnatin tarayya, yawan cibiyoyin lafiya da ke amfana da asusun BHCPF zai ƙaru daga 8,800 zuwa 13,000 a fadin ƙasar. Wannan karin yawan cibiyoyin zai taimaka wajen faɗaɗa damar samun kula da lafiya ga jama’a, musamman a yankunan karkara da ke da ƙarancin kayan aiki da ma’aikatan lafiya.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version