Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta yi kira ga ’yan ƙasarta da ke Venezuela da su gaggauta ficewa daga ƙasar. Ta ce kiran na da nasaba da rahotannin barazanar tsaro da ke ƙara ta’azzara a sassan ƙasar.

A cewar sanarwar, an samu rahotannin wasu ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai na tare hanyoyi tare da binciken motocin Amurkawa da na mutanen ƙasashen da ke goyon bayan Amurka. Wannan lamari, a cewar ma’aikatar, na barazana ga lafiyar ’yan ƙasarta a Venezuela.

Sanarwar ta zo ne mako guda bayan sojojin Amurka sun kai hari a Venezuela tare da kama shugaban ƙasar, Nicolas Maduro, da matarsa, inda aka kai su Amurka domin gurfanar da su a kotu. Shugaba Donald Trump ya ce Amurka ce ke jagorantar al’amuran ƙasar tare da gwamnatin rikon ƙwarya, duk da cewa har yanzu makusantan Maduro ne ke iko da jami’an tsaron ƙasar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version