A Amurka, wata kotu ta yanke wa ɗan Najeriya Oluwaseun Adekoya, wanda ake kira Legendary, hukuncin ɗaurin shekaru 20 a gidan yari, bayan tabbatar da shi da laifin zambar kuɗi da suka kai dala miliyan biyu. An kama shi tun farkon shekarar nan, inda tawagar masu taimaka wa alƙali suka gano cewa ya jagoranci wata babbar ƙungiyar masu satar bayanai da zambatara bankuna a faɗin ƙasar.
Adekoya mai shekara 40 ya amsa laifukan haɗa baki, satar bayanan mutane, halasta kuɗin haram, da wasu laifuka tara. Kamar yadda aka tabbatar, ya dinga amfani da bayanan jama’a na fili domin gano masu dukiya, yana sace lambobin asusu da lambar ɗan ƙasa, ta shafukan intanet irin su Telegram. Daga nan sai ya miƙa bayanan ga ƙungiyar masu amfani da takardun bogi domin fitar da kuɗaɗe daga asusun mutanen da aka zalunta.
Ana sa ran Adekoya zai biya diyyar dala miliyan 2.2 bayan kammala zaman kurkukun nasa, sannan a mayar da shi Najeriya. Rahotanni sun ce tun Disamba 2023 ne hukumar FBI ta cafke shi, inda ta kwace kayayyakin alfarma da dama ciki har da agogon Rolex, zoben aure mai darajar dala 51,000, jakunkuna, takalma da kuma kuɗi kusan dala 26,000 a asusunsa.
Hukumomin Amurka sun ce hukuncin da aka yanke zai zama izina ga masu zambar kuɗaɗe da ke amfani da hanyoyin zamani wajen cutar da mutane, tare da tabbatar da cewa duk waɗanda ke aikata irin waɗannan laifuka za su fuskanci hukunci mai tsanani.


