An yanke wa wasu mutane biyar hukuncin shekaru 21 a gidan yari saboda laifin safarar miyagun kwayoyi a Legas, kamar yadda Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Kwayoyi (NDLEA) ta bayyana. An kama uku daga cikin su – Olasupo Michael Oladimeji, Muaezee Ademola Ogunbiyi da Sola Adegoke – a filin jirgin saman Murtala Muhammad bayan an gano kilogiram 17.9 na koken da aka boye cikin kayan dinki da tsafin gargajiya da nufin kaiwa Sydney a Australia.
Bincike ya kai ga gano karin kilogiram 20.5 na nau’in tabar wiwi mai ƙarfi (Canadian Loud) a gidan Ogunbiyi da kuma kwace motar Range Rover daga gidan Adegoke a Ikeja GRA. An gurfanar da su a gaban Mai Shari’a Musa Kakaki, inda suka amsa laifukansu, sannan aka yanke musu hukuncin shekaru biyar-biyar kowannensu ba tare da zabin biyan tara ba, tare da kwace motocinsu ga Gwamnatin Tarayya.
A wani sabon batu, hukuma ta kama wasu mutane biyu, Obunike Obichukwu da Uzorchukwu Chukwurah, bisa yunkurin fitar da kilogiram 2.60 na koken da 27.90 na tramadol zuwa Gabon ta filin jirgin saman Legas. Sun amsa laifin, inda Mai Shari’a Ambrose Lewis-Allagoa ya yanke musu hukuncin shekaru uku a kurkuku tare da zabin biyan Naira miliyan biyu kowannensu madadin zaman gidan yari.
NDLEA ta ce wadannan hukuncin na nuna sabon salo na hukumar na bibiyar manyan masu daukar nauyi da masu kudi da ke bayan harkar miyagun kwayoyi, ba kawai masu safara a hannu ba. Hukumar ta ce za ta ci gaba da bin diddigi da kwace dukiyoyin da ake samu ta haramtacciyar hanya domin karya karfin kungiyoyin masu safarar kwayoyi a kasar da wajen iyaka.
