Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya mayar da martani mai zafi ga shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya yi ikirarin cewa zai kai wa Najeriya hari saboda zargin kisan Kiristoci a ƙasar. Barau ya bayyana kalaman Trump a matsayin wadansu maganganu marasa ladabi da kuma sabawa dokar ƙasa da ƙasa, yana mai cewa ba Amurka ce za ta yi wa wata ƙasa hukunci kai tsaye ba tare da bin matakan Majalisar Ɗinkin Duniya ba.
Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) da ƙungiyar makiyaya, Miyetti Allah (MACBAN), su ma sun soki kalaman Trump, suna masu zargin Amurka da neman yin katsalandan cikin harkokin cikin gida na Najeriya. NEF ta ce Amurka tana da tarihin lalata kasashe da sunan taimako, tana kawo misalai da Iraq, Libya da Afghanistan. A nasa ɓangaren, Miyetti Allah ta karyata zargin cewa tana da alaƙa da ta’addanci, tana mai cewa an yi amfani da sunansu ne wajen siyasa da yi wa Arewa ƙarfen hannu.
Sannan kungiyar matasan Arewa, AYCC, ta ce barazanar Trump ba don kare Kiristoci ba ce kamar yadda yake fada, sai dai tana da alaka da sha’awarsa ga albarkatun Najeriya da kuma tsarin dangantaka da ƙasashen duniya. Sun yi gargadi cewa duk wani yunkurin mamayar Amurka zai haifar da ɗumbin tashin hankali da wahala ga talakawan ƙasar.
A ƙarshe, dukkan manyan kungiyoyin Arewa sun bayyana cewa Najeriya ƙasa mai cikakken ikon kanta ce, kuma tana da damar warware matsalolinta ba tare da katsalandan ba. Sun bukaci gwamnatin tarayya ta ɗauki matakan diflomasiyya cikin gaggawa, tare da jan hankalin Amurka cewa abu mafi dacewa shi ne tattaunawa da mutunta dokokin duniya.
