Hukumar Kwastam ta Najeriya ta ce ta kama wata tankar man fetur mai ɗauke da lita 60,000 da ake zargin an karkatar da ita daga rabon cikin gida zuwa wani yankin iyaka a jihar Katsina. An ce jami’an rundunar Operation Whirlwind ne suka kama tankar a kan titin Jibia, inda aka gano cewa takardun da ke tare da motar na karya ne kuma ba su cika sharuddan jigilar man ba.

Shugaban rundunar ta musamman, Kola Oladeji, wanda aka wakilta ta hannun Sa’ad Isah-Yahaya, ya bayyana cewa wannan samame ya fito ne daga matakan gwamnati na dakile fitar da man fetur ta bayan fage zuwa kasashen makwabta. Ya ce wannan abu na iya janyo wa tattalin arzikin ƙasa babbar hasara, musamman ganin an sayi man da tallafin gwamnati ne domin amfani a cikin gida.

Hukumar ta ce tana da niyyar ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin da ke sa ido a harkar man fetur domin tabbatar da tsaro da daidaito a tsarin rarraba makamashi a Najeriya. An kuma mikawa Hukumar Kula da Masana’antar Man Fetur ta Tsakiya da Kasa (NMDPRA) tankar da aka kama domin cigaba da bincike da daukar mataki.

A nasa jawabin, kwamishinan NMDPRA na Katsina, Mohammed Omar, ya jinjinawa Kwastam bisa kulawa da sa ido, yana mai cewa hadin gwiwar hukumomi na da matukar muhimmanci wajen dakile safarar man fetur da sauran ayyukan da ke ruguzar tattalin arziki. Ya ce hukumar ta kuduri aniyar tabbatar da tsafta da ingantaccen rahoto a bangaren rarraba man fetur a kasa.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version