Wani jami’in Hukumar Civil Defence (NSCDC) mai mukamin Deputy Superintendent, Sani Yakubu, ya amsa laifin karkatar da kuɗi har N1.7 miliyan da aka damƙa masa, a gaban babbar kotun jihar Kaduna. Hukumar ICPC ce ta gurfanar da shi gaban Mai Shari’a Isiaka, bisa zargin cin amanar aiki da sace kuɗin wata mata mai suna Vennica Idoko, da aka bai wa jami’in domin ya karɓa a madadinta.
A cewar bayanan da ke cikin ƙarar, an zargi Yakubu da karkatar da kuɗin ne yayin da yake aiki a matsayinsa na jami’in NSCDC, alhali kuma an damƙa kuɗin ne a ƙarƙashin amana. Laifukan sun sabawa sassan 294, 300, da 86 na Dokar Penal Code ta Jihar Kaduna. An bayyana cewa ya karɓi kuɗin a matsayin wakili amma ya yi amfani da su zuwa ga bukatunsa na kansa.
Rahotanni sun nuna cewa yayin zaman shari’ar, jami’in ya fashe da kuka tare da amsa laifi a kan dukkan tuhumar da ICPC ta gabatar. Bayan haka ne mai shari’a ya dage ci gaban shari’ar zuwa ranar 12 ga Nuwamba, 2025, domin yanke hukunci da bayyana hukuncin da zai fuskanta.
Hukumar ICPC ta gargadi ma’aikatan gwamnati da cewa duk wanda ya yi amfani da mukaminsa wajen cutarwa ko cin amana zai fuskanci hukunci. Ta ce irin wannan lamari na rage wa jama’a amincewa da hukumomin gwamnati, don haka za ta ci gaba da bibiyar dukkan ayyukan cin hanci da rashawa.
