Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ƙasa (ASUU) ta sanar da fara yajin aikin gargaɗi na tsawon mako biyu a dukkan jami’o’in gwamnati a Najeriya. Shugaban kungiyar, Farfesa Chris Piwuna, ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai da aka gudanar a jami’ar Abuja ranar Lahadi 12 ga Oktoba. Wannan mataki ya biyo bayan ƙarewar wa’adin gargadin kwanaki 14 da kungiyar ta bayar tun ranar 28 ga Satumba, 2025.
ASUU ta umarci dukkan rassanta a fadin ƙasar da su daina aiki daga tsakar daren Litinin, 13 ga Oktoba, 2025. Farfesa Piwuna ya bayyana cewa yajin aikin zai kasance cikakke kuma gaba ɗaya, kamar yadda majalisar zartarwa ta ƙasa ta amince a taronta na baya-bayan nan. Wannan na nuna sabon takaddama tsakanin ASUU da Gwamnatin Tarayya duk da tattaunawar sulhu da ake yi domin kauce wa sake shiga rikicin ilimi.
A cewar Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na ƙoƙarin kammala tattaunawa da ASUU da sauran ƙungiyoyi don warware matsalolin da suka dade suna jawo rikici. Ya bayyana cewa gwamnati ta riga ta saki Naira biliyan 50 domin biyan hakkokin EAA ga malamai, sannan an ware karin biliyan 150 a kasafin kuɗin 2025 don gyaran jami’o’i, wanda za a rarraba a matakai uku.
Sai dai duk da wannan ci gaban, ASUU ta dage cewa babu wani mataki tabbatacce da zai iya dakatar da su daga aiwatar da shawarar yajin aiki. Wannan sabon yajin aikin na iya jefa harkar ilimi cikin wani sabon cikas, yayin da ɗalibai da iyaye ke fargabar tasirin da hakan zai haifar a tsarin karatun jami’o’in gwamnati.
