Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wasu matasa biyar, ciki har da ango da amarya, bisa zargin gudanar da auren bogi ba tare da amincewar iyaye ba. Mataimakin Kwamanda Janar na hukumar, Dr Mujahideen Aminuddeen, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Kano ranar Litinin 13 ga Oktoba. Ya ce cikin wadanda aka kama akwai wakilai biyu da shaidar aure daya.
Rahotanni sun nuna cewa an kulla wannan aure ne da sadaki na Naira 10,000, wanda ya gaza ka’idar da shari’ar Musulunci ta tanada. Aminuddeen ya ce hakan ya saba wa tsarin aure na Musulunci da kuma ka’idojin doka, don haka hukumar ta fara bincike kan lamarin.
Ya bukaci iyaye da su kara kulawa da harkokin zamantakewar ’ya’yansu, musamman a lamuran da suka shafi aure, don kauce wa irin wannan sabawa doka da addini. Hukumar ta ce za ta ci gaba da daukar matakai masu tsauri domin tabbatar da bin ka’idojin aure yadda ya kamata.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamnatin Jihar Kano ta umurci hukumar Hisbah da ta fara shirye-shiryen auren gata na mutum 2,000 da za a gudanar. Ana bukatar dukkan wadanda ke son shiga wannan shiri su yi rajista tare da yin gwajin lafiya kafin a daura aure.
