Kamfanin Dangote Cement ya kaddamar da sabuwar masana’antar siminti a Attingué, kimanin kilomita 30 daga birnin Abidjan na ƙasar Côte d’Ivoire. An gudanar da bikin kaddamarwar ne a ranar Laraba a otal ɗin Novotel Abidjan-Marcory, tare da bayyana cikakkun bayanai ta bakin Manajan Darakta na kamfanin a ƙasar, Serge Gbotta.

Masana’antar, wacce ke kan fili mai faɗin hekta 50, tana da ƙarfin samar da ton miliyan uku na siminti a duk shekara, lamarin da ya sanya ta zama ɗaya daga cikin manyan wuraren samar da siminti na kamfanin a wajen Najeriya. An kashe kusan CFA biliyan 100 wajen gina ta, domin cikar burin Aliko Dangote na gina nahiyar Afirka mai ƙarfin masana’antu da rage dogaro da kayayyakin waje.

Sabuwar masana’antar ta sanya Côte d’Ivoire ta zama ƙasa ta 11 a nahiyar da ke da masana’antar Dangote Cement, inda gaba ɗaya ƙarfin samarwar kamfanin ya kai ton miliyan 55 a kowace shekara. Kamfanin ya ce wannan mataki zai taimaka wajen gina manyan ayyukan raya ƙasa da kuma biyan buƙatar gina gine-gine da ke ƙaruwa a ƙasar sakamakon bunƙasar birane.

Bugu da ƙari, masana’antar za ta samar da fiye da ayyukan yi 1,000 kai tsaye, musamman ga matasa da ƙananan kamfanoni kamar masu jigila, dillalai da masu sana’o’in gine-gine. Shugaban kamfanin Dangote Cement a Côte d’Ivoire ya ce burinsu shi ne samar da siminti mai ingancin ƙasa da ƙasa a farashi mai sauƙi ga ‘yan ƙasar, tare da ba da gudunmawa ga ci gaban al’umma.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version