Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya aike da saƙon taya murna ga tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yayin da yake cika shekaru 69 a duniya.
A cikin saƙonsa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Atiku ya bayyana cewa jajircewar Kwankwaso wajen hidimar jama’a, ilimi da ci gaban ƙasa na ci gaba da zama abin koyi ga al’umma daga ƙarni zuwa ƙarni. Ya ce irin gudunmawar da Sanatan ke bayarwa wajen inganta rayuwar talakawa da gina ƙasa abin yabo ne.
Atiku ya kuma taya Kwankwaso, iyalansa, abokansa da magoya bayansa murna a wannan rana ta musamman, tare da yi masa fatan alheri da ƙara lafiya, ƙoshin jiki da ɗorewar nasara a rayuwarsa da ayyukansa na gaba.
