Ministan ci gaban matasa na ƙasa, Ayodele Olawande, ya ce babu wata gwamnati ta jiha da za ta iya gudanar da al’amuranta yadda ya kamata ba tare da gudummawar ‘yan bautar ƙasa na NYSC ba. Ya bayyana haka ne a taron masu ruwa da tsaki kan sauye-sauyen da ake shirin gudanarwa cikin hukumar NYSC a Abuja.
A jawabin da ya gabatar, Olawande ya ce shirin NYSC ya shafe shekaru sama da 50 yana taka muhimmiyar rawa wajen haɗa kan matasa da tallafa wa ci gaban ƙananan hukumomi, musamman a fannoni kamar ilimi, kiwon lafiya, noma, da wasanni. Ya kuma ce lokaci ya yi da ya kamata a sabunta tsarin, domin ya dace da sauye-sauyen zamani da bukatun ƙasa. A cewarsa, akwai bukatar a sake tsarin tura masu bautar ƙasa domin a daidaita su da kwararrun fannoni da suka kware a kai.
Darakta janar na NYSC, Birgediya Janar Olakunle Nafiu, ya bayyana cewa hukumar na tura kusan matasa 400,000 kowace shekara, kuma ana sa ran adadin zai ƙaru zuwa 650,000 a 2026. Ya ce wannan gudummawa ta NYSC na taimaka wa jihohi rage sama da biliyan ₦30 zuwa ₦40 a duk shekara, inda ma a Abuja ake samun likitoci 400 daga cikin masu bautar ƙasa duk shekara domin cike gibi. Wannan, a cewarsa, na daga cikin dalilan da yasa babu wata jiha da za ta iya tafiya lafiya ba tare da NYSC ba.
