Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya kakaba dokar takunkumin fita na awanni 24 a Ƙaramar Hukumar Lamurde bayan sake barkewar tashin hankalin ƙabilanci da aka samu a daren Lahadi. Sanarwar da aka fitar ta hannun Sakataren Yaɗa Labarai na Mataimakin Gwamna, Hussaini Hammangabdo, ta tabbatar da cewa an umarci jami’an tsaro su shiga yankin nan take don dawo da doka da oda.

Gwamnan ya jaddada cewa dole ne jami’an tsaro su garzaya cikin yankunan da ake fargabar rikici don dakile yaduwar tashin hankali da kuma tabbatar da zaman lafiya. Ya ce gwamnati ba za ta lamunci duk wani abu da zai haifar da sabon rikici ko barna ba, musamman duba da yadda rikicin ya fara bazuwa kafin karshen mako.

A cikin ƙoƙarin kawo ƙarshen fitinar, gwamnati ta roƙi mazauna Lamurde da su kasance cikin nutsuwa, tare da ba da cikakken haɗin kai ga jami’an tsaro. Wannan mataki, a cewar rahotannin da Bechi Hausa ke bibiyarsu, na nufin hana rikicin ya ƙara ta’azzara da kuma kare rayuka da dukiyoyi.

Gwamnatin jihar ta kuma yi alƙawarin ci gaba da sa ido kan lamarin tare da ɗaukar duk matakan da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa. Ta kuma jaddada cewa an ɗauki wannan mataki ne domin samar da kwanciyar hankali a yankin da ya dade yana fama da rikice-rikicen al’umma.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version