Kamfanin TikTok ya sanar da dakatar da damar amfani da fasalin watsa shirye-shirye kai tsaye (LIVE) ga masu amfani a Najeriya a tsakanin karfe 11 na dare zuwa 5 na safe, bisa wani bincike na tsaro da kamfanin ke gudanarwa.

Masu amfani sun karɓi sanarwa ta cikin app a ƙarshen mako, wacce ta bayyana cewa dakatarwar na cikin wani bincike domin tabbatar da tsaro da kariya ga al’umma. TikTok bai fadi cikakken bayani ba kan yadda binciken zai ƙare ko tsawon lokacin da za a ci gaba da matakin.

Wannan mataki na zuwa ne bayan ‘yan makonni da kamfanin ya fitar da sabbin kididdigar tsaro a Yammacin Afirka, inda a zangon biyu na shekarar 2025, TikTok ta dakatar da 2,321,813 na zaman LIVE da 1,040,356 masu watsa shirye-shirye a duniya saboda karya ka’idojin Monetisation na LIVE. A Najeriya kadai, an dakatar da zaman LIVE 49,512 a wannan lokaci.

Har ila yau, TikTok ya cire bidiyo 3,780,426 a Najeriya daga Afrilu zuwa Yuni 2025 saboda karya Ka’idojin Al’umma, inda kashi 98.7% aka cire su kafin a kalla, kuma kashi 91.9% aka cire cikin awanni 24.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version