Sabbin hafsoshin tsaron Najeriya sun sha alwashin sake fasalin tsarin tsaro ta hanyar ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙasashen waje, ƙera makamai a cikin gida, da inganta walwalar sojoji domin kawo ƙarshen ta’addanci da rashin tsaro a ƙasar. Wannan alkawari ne suka bayar yayin da Majalisar Dattawa da ta Wakilai ke tantance su a zaman da aka gudanar a ranar Laraba a Abuja.
Babban hafsan tsaro, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya bayyana cewa lokaci ya yi da Najeriya za ta daina dogaro da kasashen waje wajen siyan kayan yaki. Ya ce zai mayar da hankali kan ƙirƙirar masana’antun tsaro na cikin gida, tare da tabbatar da kyakkyawar rayuwar jami’an tsaro da iyalansu.
Shugaban rundunar sojin ƙasa, Manjo Janar Waidi Shuaibu, ya yi alkawarin sabunta dabarun yaki da ƙarfafa horar da dakaru, inda ya tuna yadda ya jagoranci ceto wasu daga cikin ‘yan matan Chibok a baya. Haka nan, shugaban rundunar ruwa Rear Admiral Idi Abas ya bayyana cewa za su yi amfani da fasahar zamani da jiragen sintiri (drones) wajen yaki da fashi da makami, satar mai da kuma garkuwa da mutane a teku.
A nasa bangaren, shugaban rundunar sama, Air Vice Marshal Kennedy Aneke, ya ce zai yi aiki da jajircewa da kirkira don tabbatar da tsaron sama. Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya ce tantancewar ta tabbatar da cewa kawai ƙwararru da masu kishin ƙasa ne za su jagoranci rundunonin tsaro. Ana sa ran shugaban ƙasa Bola Tinubu zai karrama sabbin hafsoshin a fadar shugaban ƙasa, bayan amincewar majalisun biyu da nadin nasu.
