Babban layin wutar lantarki na ƙasa ya sake rushewa a ranar Alhamis, lamarin da ya jefa sassan Najeriya cikin duhu tare da katse wutar lantarki ga miliyoyin gidaje da kasuwanci. Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya tayar da hankalin jama’a da masu sana’o’i a faɗin ƙasar.
Bincike ya nuna cewa samar da wutar lantarki ya faɗi daga sama da megawatt 4,500 zuwa megawatt 24 kacal da misalin ƙarfe 1:30 na rana. Dukkan tashoshin samar da wuta guda 23 da ke da alaƙa da grid ɗin sun daina fitar da wuta, lamarin da ya haifar da rabon sifili ga kamfanonin rarraba wuta guda 11.
Har zuwa lokacin fitar da rahoton, ba a gano musabbabin rushewar ba, kuma kamfanin Transmission Company of Nigeria bai fitar da cikakken bayani ba. Wannan ne karon farko da grid ɗin ya rushe a shekarar 2026, bayan makamancin haka da ya faru a ranar 29 ga Disamba 2025, wanda ya haddasa matsalar wuta a ƙasar.
