Babban Bankin Duniya ya sanya ranar Disamba 16, 2025 a matsayin ranar da zai yanke hukunci kan amincewa da sabon rancen dala biliyan ɗaya ($1bn) da Najeriya ta nema domin tallafawa ci gaban tattalin arziki da samar da ayyukan yi. Sabon rancen, wanda ake kira Nigeria Actions for Investment and Jobs Acceleration, zai haɗa da rabin kuɗin daga Hukumar Ci Gaban Kasa (IDA) da rabin daga Bankin Gyara da Cigaba (IBRD). A cewar bankin, an tsara wannan tallafin ne don ƙarfafa gyare-gyaren tattalin arziki, buɗe damammakin saka jari, da ƙara ayyukan yi a sassan noma, kasuwanci, da fasahar zamani.

Bankin ya bayyana cewa rancen zai taimaka wajen matsar da Najeriya daga matakin “daidaita tattalin arziki” zuwa “ci gaban da ke amfani ga kowa,” tare da mayar da hankali kan sauƙaƙa hanyoyin kasuwanci da rage tsadar rayuwa. A karkashin shirin, za a inganta damar samun bashi, haɓaka kasuwannin hannayen jari, da aiwatar da dokar Digital Economy and E-Governance Bill 2025, wacce za ta kafa tsarin gwamnati na zamani. Haka kuma za a goyi bayan amfani da yarjejeniyar AfCFTA don rage haraji da sauƙaƙa fitar da kayayyaki zuwa kasashen Afirka.

Rancen zai kuma taimaka wajen rage hauhawar farashin kayayyaki da inganta samar da abinci ta hanyar ci gaba da noman zamani, musamman a amfanin gona kamar shinkafa, masara da wake. A cewar Bankin Duniya, tsarin zai iya samar da dubban ayyukan yi kai tsaye, musamman ga matasa da ƙananan manoma. Haka kuma, za a ƙara samun ragin haraji da sauƙin shigo da kayan masarufi, abin da zai taimaka wajen rage farashin kayayyaki ga jama’a da ƙarfafa kasuwancin cikin gida.

Ana sa ran kuɗin za su fito cikin matakai biyu bayan Najeriya ta cika wasu sharuddan manufofi, inda Ma’aikatar Kuɗi tare da Babban Bankin Najeriya (CBN) za su kula da aiwatar da shirin. Wannan sabon rance zai zama ɗaya daga cikin manyan tallafin manufofi da Bankin Duniya ya taba bayarwa ga Najeriya a ‘yan shekarun nan. A halin yanzu, Bankin Duniya ne babban mai ba Najeriya bashi, inda yake da kaso fiye da 41% na bashin ƙasar waje, wanda ya kai dala biliyan 19.39 daga jimillar dala biliyan 46.98 da akebin ƙasar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version