Ƙungiyar shugabannin jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) na jihohi 37 ta sake jaddada cewa tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, yana nan a karkashin haramcin shekaru 30 daga shiga jam’iyyar. Wannan sanarwa ta fito ne bayan jita-jitar cewa El-Rufai na shirin komawa cikin jam’iyyar kafin babban taron kasa mai zuwa. Shugaban ƙungiyar, Femi Olaniyi, ya bayyana a wani taron manema labarai a Abuja cewa hukuncin da kwamitin gudanarwa na ƙasa ya yanke kan El-Rufai ba zai canza ba, yana mai cewa an kore shi bisa ka’ida kuma har yanzu ana kan wannan hukunci.

Olaniyi ya ce El-Rufai ya shiga jam’iyyar ne ta “ƙofa ta baya,” ba bisa tsarin jam’iyyar ba. Ya tunatar da cewa tun a watan Afrilu 2025 an bayyana cewa duk wanda yake son shiga SDP dole ne ya bi matakin gunduma da jiha kafin ya zama ɗan jam’iyya na gaskiya. A cewarsa, abin da El-Rufai ya aikata a cikin tsarin jam’iyyar ya saba wa dokokin cikin gida, kuma an tabbatar da hukuncin korarsa da cikakken goyon bayan shugabannin jihohi.

Rahotanni sun nuna cewa wannan rikicin ya raba jam’iyyar SDP gida biyu, inda bangaren shugabannin jihohi ke kiran a “yi wa jam’iyyar tiyata” domin cire abin da suka kira “cutar Gabamism” — wato bangaren da ke goyon bayan tsohon shugaban jam’iyyar na ƙasa, Shehu Gabam, wanda shi ma aka dakatar. Bangaren Gabam kuwa ya dage cewa dakatarwar ba a bisa ƙa’ida take ba, abin da ke nuna cewa rikicin zai iya kaiwa kotu.

Tsohon gwamnan, wanda bai yi tsokaci kan lamarin ba har zuwa lokacin da aka wallafa rahoton, an zarge shi da amfani da takardun bogi, da kuma ƙoƙarin karkatar da tsarin jam’iyyar ta hanyoyi da ba su da izini. Hukumar gudanarwa ta jam’iyyar ta bayyana cewa El-Rufai ba zai iya shiga ko hulɗa da SDP ba har tsawon shekaru 30 masu zuwa.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version