Fitaccen ɗan kwallon ƙasar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya bayyana cewa gasar cin Kofin Duniya ta 2026 ita ce za ta zama ta ƙarshe a aikinsa na wasa. Ya ce a lokacin zai kai shekara 41, kuma ya an ganin lokaci ya yi da ya kamta ya koma gefe bayan shekaru kusan 25 yana haskakawa a duniyar ƙwallon ƙafa. Ronaldo, wanda ya ci fiye da kwallaye 950, ya ce yanzu yana jin dadin wasansa.
Ronaldo ya yi wannan furuci ne yayin tattaunawa ta bidiyo a wani taron zuba jari da yawon bude ido da aka shirya a Saudiyya. Ya ce duk da yana da cikakkiyar lafiya, amma yana jin ƙarfin jikinsa yana raguwa sannu a hankali. Ya ce zai cigaba da taka leda na shekara ɗaya zuwa biyu kafin ya yi bankwana da filin wasa gaba ɗaya. A cewarsa: “Na bayar da komai ga ƙwallon ƙafa, yanzu lokaci ne na jin daɗin karshe.”
Ya kuma tabo batun ɗansa, Cristiano Jr., wanda ke buga wa ƙungiyar matasa ta Portugal U-16. Ronaldo ya ce ba ya son ɗansa ya ji matsin cewa dole ya zama kamar shi. Ya jaddada cewa mafi muhimmanci shi ne yaron ya kasance cikin farin ciki, ko ya zabi ƙwallon ƙafa ko wata hanya daban. Ya ce shi fa zai kasance ginshikin goyon bayansa.
Portugal tana dab da lashe tikitin zuwa Kofin Duniya na 2026 wanda za a yi a Amurka, Kanada da Mexico. Ronaldo ya taba zuwa kusa da lashe Kofin Duniya a 2006 lokacin da France ta cire Portugal a wasan kusa da na ƙarshe. Idan Portugal ta samu gurbin 2026, wannan za ta zama gasar Kofin Duniya ta shida ga Ronaldo.
