Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi, ya ce bai ji tsoron cewa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, zai karɓe tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ba a zaɓen 2027. Obi ya bayyana haka ne yayin wata hira da jaridar Sunday PUNCH a Abuja, inda ya bayyana Atiku a matsayin “babba kuma jagora.”

Maganganunsa na zuwa ne bayan rahotanni da ke nuna cewa magoya bayan Atiku daga jam’iyyar PDP na komawa cikin hadakar ADC, abin da ya jefa magoya bayan Obi cikin fargabar yiwuwar Atiku ya mamaye jam’iyyar. Hakan ya ƙara tayar da ƙura bayan maganar da Atiku ya fada a wata hira da BBC Hausa cewa ba zai ja daga takara ba sai dai idan aka kayar da shi a zaben fidda gwani na ADC. Tsohon sanata Shehu Sani ma ya gargadi cewa zai zama da wahala a kayar da Atiku idan ya shiga kowace jam’iyya.

Sai dai Obi ya bayyana cewa hadakar ADC ba fagen gasa ba ce, illa wani yunƙuri na haɗa ƙarfi don ceto ƙasa. Ya ce, “Atiku babban ɗan uwa ne kuma jagora. Ni mamba ne na jam’iyyar Labour kuma ina cikin hadakar da ke samar da ADC don zaɓen 2027. Dukkanmu za mu haɗu a matsayin mutane masu kishin ƙasa domin yin abin da ya dace.” Ya kuma nuna cewa yana da niyyar tsayawa takara, yana mai cewa cancanta da iya aiki su ne abin dubawa wajen zaɓar shugaba mai zuwa.

Obi ya jaddada cewa yana da ƙwarewa da ƙudurin sauya tafiyar Najeriya cikin shekaru huɗu. Ya kuma kira ’yan Najeriya da su mayar da hankali kan manufofi da walwalar al’umma maimakon jam’iyyu kawai. Obi da Atiku duka sun sha kaye a hannun Bola Tinubu a zaɓen 2023, wanda ya kasance ɗaya daga cikin mafi zafi a tarihin dimokuraɗiyyar Najeriya.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version