Jam’iyyar Labour Party (LP) ta sake hura wutar rikici kan haɗin gwiwar ‘yan adawa kafin babban zaɓen 2027, inda ɓangaren jam’iyyar da ke goyon bayan Peter Obi da Gwamnan Abia, Alex Otti, ya bayyana cewa haɗin kai ne kaɗai zai iya kawar da Shugaba Bola Tinubu daga mulki. Kakakin wucin gadin jam’iyyar, Prince Tony Akeni, ya roƙi tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, da ya ajiye burin takara ya mara wa Obi baya idan da gaske yana son ceto Najeriya daga halin da take ciki.
Akeni ya bayyana cewa idan Atiku ya nuna ƙauna ga ƙasar ta hanyar goyon bayan Obi, za a iya samun nasara cikin sauƙi a 2027, yana mai cewa Tinubu “shine shugaban ƙasa mafi sauƙin dokewa a duniya” muddin ‘yan adawa suka haɗa kai. Ya yi gargadin cewa rashin haɗin kai tsakanin manyan ‘yan adawa ne ke ba jam’iyyar APC damar ci gaba da lashe zaɓe.
Ya kuma soki gwamnatin Tinubu da cewa gwamnati ce mai cika da son kai da yawan sauya sheka, yana mai cewa hakan zai iya haifar da rikici a cikin jam’iyyar mai mulki. A cewarsa, “Tinubu yana ɗauke da abin da zai rushe masa jam’iyya saboda yawan ‘yan siyasar da ke neman matsayi ga cikin kwadayin da ya yi yawa.” Akeni ya yabawa Obi, yana kwatanta shi da tsohon Firayim Ministan Singapore, Lee Kuan Yew, saboda jagoranci cikin hangen nesa da gaskiya.
Sai dai Atiku ya musanta batun janye wa Obi, yana mai cewa ya fi dacewa a samar da haɗin gwiwar jam’iyyun adawa da za su tantance jagora ta hanyar tattaunawa, ba ta hanyar sadaukar da kai ba. A gefe guda kuma, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar LP, Ayo Olorunfemi, ya ce babu wani hatsarin rushewar dimokuraɗiyya ko kafa jam’iyya ɗaya, yana mai cewa ‘yan Najeriya ne suka zabi halin da suke ciki tun daga 2015. Jam’iyyar LP dai har yanzu tana fama da rikicin cikin gida tsakanin ɓangaren Julius Abure da na Obi-Otti yayin da take shirin fafatawa a zaben 2027.
