Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fitar da dala biliyan 1.259 a watanni uku na farko na shekarar 2025 domin tallafa wa ‘yan kasuwar da ke shigo da man fetur da sauran kayayyakin mai, duk da cewa masana’antar Dangote ta fara samar da man cikin gida. Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙoƙarin rage dogaro da shigo da mai daga ƙasashen waje.

Rahoton Hukumar NMDPRA ya nuna cewa, duk da karuwar samar da mai daga masana’antar Dangote, ‘yan kasuwa sun shigo da kusan kashi 69 cikin 100 na man da aka ƙone a ƙasar tsakanin watan Agusta 2024 da farkon Oktoba 2025. CBN ta bayyana cewa dala miliyan 457.83 aka fitar a Janairu, sai ta sauka zuwa dala miliyan 283.54 a Fabrairu, sannan ta haura zuwa dala miliyan 517.55 a watan Maris – wanda ya fi sauran watanni yawan kuɗi.

A cewar Kungiyar Dillalan Man Fetur ta IPMAN, dalilin da yasa ƴan kasuwa ke ci gaba da shigo da mai shi ne bambancin farashi. Kakakin ƙungiyar, Chinedu Ukadike, ya bayyana cewa ‘yan kasuwa na sayen mai daga inda suka fi samun riba, ko daga wajen Dangote ne ko kuma daga ƙasashen waje, domin farashin ne ke tantance kasuwa.

Sai dai masana sun ce wannan shirin na CBN yana nuna sauyi a kasuwar man fetur, inda ake ganin matakan rage shigo da mai daga waje suna ƙara karɓuwa. Rahoton ƙarshe daga ƙungiyar MEMAN ya kuma nuna raguwar farashin shigo da lita ɗaya na man fetur zuwa N805.46, sakamakon sauyin farashin danyen mai da kuma canjin kudin waje.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version