Alhaji Aliko Dangote, Shugaban Kamfanin Dangote Industries Limited, ya yi kira da a gudanar da bincike kan Shugaban Hukumar NMDPRA, Injiniya Farouk Ahmed, bisa zargin abin da ya kira lalata tattalin arzikin Najeriya ta hanyar ci gaba da ba da lasisin shigo da man fetur duk da karuwar tace mai a cikin gida. Dangote ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya gudana a ranar Lahadi, 15 ga Disamba 2025, a matatar man Dangote da ke Legas.
Dangote ya ce matakan NMDPRA na hana masana’antar tace mai ta cikin gida bunƙasa, inda ya zargi hukumar da ba da lasisin shigo da kusan lita biliyan 7.5 na PMS domin zangon farko na shekarar 2026. Ya ce hakan na ƙara dogaro da shigo da fetur daga waje tare da kassara masu zuba jari a fannin tace mai na cikin gida. Dangote ya kuma bayyana zargin cewa Shugaban NMDPRA na rayuwa fiye da yadda albashinsa ya kamata, inda ya ambaci cewa ‘ya’yansa huɗu na karatu a makarantu masu tsada a Switzerland.
Ya ce bai nemi a kori Injiniya Ahmed ba, sai dai a yi masa cikakken bincike daga hukumomin da suka dace kamar Hukumar Code of Conduct Bureau, yana mai cewa a shirye yake ya gabatar da hujjoji. Dangote ya kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa farashin fetur zai ƙara sauka, inda ya sanar da cewa daga ranar Talata mai zuwa, litar PMS za ta rika sayuwa ba fiye da ₦740 ba a Legas, bayan rage farashin matatar zuwa ₦699. Ya ƙara da cewa matatar Dangote mallakin ‘yan Najeriya ce, kuma za a jera ta a kasuwar hannayen jari ta Najeriya domin bai wa jama’a damar mallakar hannun jari a cikinta.
