Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Kano Municipal, Hon. Injiniya Sagir I. Koki, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) a cikin wata wasikar da ya aikawa shugabar gundumar Zaitawa a ranar 11 ga Nuwamba, 2025. Ya ce matakin nasa ya biyo bayan hakkinsa na doka bisa sashe na 40 na kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma tanadin kundin tsarin NNPP.
A cewarsa, rikicin cikin gida da ya addabi shugabancin jam’iyyar a matakin ƙasa ya haifar da cikas ga aikinsa na wakiltar jama’a yadda ya dace. Koki ya ce rikicin ya sa ya zama mai wuya gare shi ya ci gaba da gudanar da ayyukansa na wakilci da bayar da ingantaccen goyon baya ga al’ummar Kano Municipal a majalisar wakilai.
Ya gode wa jam’iyyar NNPP bisa damar da ta ba shi ya yi aiki a karkashinta, yana mai jaddada cewa gogewa da haɗin kai da ya samu daga shugabannin jam’iyyar da mambobi sun kasance abin alfahari. Koki ya kuma bayyana godiyarsa ga dukkan masu ruwa da tsaki a cikin jam’iyyar tare da yi musu fatan alheri a cigaban da ke gaba.
